Isa ga babban shafi
Israel-Palestine

Za a sake nazari kan kudirin takaita kiran sallah

Majalisar dokoki a kasar Isra’ila ta ce za ta sake duba kudirin takaita kiran sallah da wani dan majalisa ya shigar a gabanta a yayin da ma’aikatar lafiyar kasar ta ce dokar za ta iya samun shiga idan aka hada da Yahudawa.

Daruruwan musulmin yankin Palisdinu a masallacin Al-aqsa da ke Jerusalem.
Daruruwan musulmin yankin Palisdinu a masallacin Al-aqsa da ke Jerusalem. middleeastmonitor.com
Talla

Dan majalisar dake jagoranci kudirin Moti Yogev, ya ce ya gabatar da kudirin ne domin takaita hayaniya cikin dare.

Sai dai Ministan lafiyar kasar Yakov Litzman, ya ce sai dai dokar ta hada da yahudawa dake kade kade na addu’o’I a wasu lokutan a tsakiyar dare.

Moti Yogev dake neman goyon bayan Litzman ya ce hana mutum baci cikin dare tamkar yi masa sata ne a dokokin Yahudawa, inda yake misali da kiran sallah da ake yi a cikin dare.

Amincewar Litzman da kudirin dokar, zai bayar da daman isar da batun gaban gwamnati a ranar lahadi da kuma majalisar kasar domin tsallake karatu na 3 a ranar laraba.

Larabawa dai sun kunshi kashi 17.5 na al’ummar Isra’ila kuma yawancinsu Falasdinawa musulmi ne a gabashin birnin Kudus da ke zargin Yahudawa na danne musu hakinsu, yayin da kungiyoyin kare hakkin bil’adama ke bayyana yunkurin a mastayin barazana ga ‘yanci gudanar da addini.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.