Isa ga babban shafi
Faransa

Tsohon ministan kudin Faransa zai tsaya takarar shugaban kasa

Emmanuel Macron ya yi alkawarin samar da tsarin Demokradiya da za ta haifar da chanji a kasar a lokacin da ya sanar da bukatar sa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a yau laraba.

Emmanuel Macron ya ce zai tsaya takarar shugabancin kasar Faransa.
Emmanuel Macron ya ce zai tsaya takarar shugabancin kasar Faransa. REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Emmanuel Macron da ya rike mukamin ministan kudin kasar a gwamnatin shugaba Francois Hollande ya sanar da bukatar tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar a matsayin dan takara mai zaman kansa.

Sanarwar tsayawa takara a matsayin dan takara mai zaman kai abune da ya zo wa jam’iyyun siyasar kasar a ba-zata musanman ‘ya ‘yan jam’iyyar Socialist ta shugaba Hollande da ke kallon yunkurin na Macron a matsayin yaudara.

Sai dai a yayin sanarwar takarar Macron ya ce siyasar kasar ta gurgunce, inda ya yi alkawalin sake farfado da ita, tare da kare masu rauni da yin adalci a tsakanin sauran al’umma.

A shekara mai zuwa za a gudanar da babban zaben shugabancin kasar Faransa inda za’a fafata a tsakanin ‘yan takara bakwai, cikinsu da tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy da Marie Le Pen ta jam’iyyar masu ra’ayin rikau, FP da tsofafin Firaiyi Minista kasar Biyu Francois Fillon da kuma Alain Juppe.

Har ya zuwa wannan lokacin Shugaba Hollande dai bai yi wata sanarwa ba ta ko zai tsaya takara ko ah ah.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.