Isa ga babban shafi
Amurka

Hillary Clinton ta zargi FBI da taka rawa a kayen da ta sha

‘Yar takarar kujerar shugabancin  Amurka Hillary Clinton da ta sha kaye a zaben da aka gudanar a makon jiya ta zargi shugaban FBI James Cormey da hannun a rage ma ta tagwamashi sanadiyar wanke ta daga aikata laifi kan batun emel daf da zaben.

Yar takarar kujerar shugabancin Amurka Hillary Clinton da ta sha kaye a zaben na makon jiya.
Yar takarar kujerar shugabancin Amurka Hillary Clinton da ta sha kaye a zaben na makon jiya. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Kwanaki biyu kafin zaben shugaban kasar ne dai shugaban hukumar FBI James Comey ya aika da wasika ga majalisar dokokin kasar na cewa hukumar ba ta sami Clinton da laifin komai ba a binciken da aka gudanar akan sakonnin imel din ta a lokacin da take aiki a matsayin sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Misis Clinton dai ba ta sami yawan kuri’u 270 da ake bukata don lashe zaben ba, al’amarin da ya bai wa abokin hammayarta Donald Trump gagarumar nasara da ya matukar bai wa al’umma na ciki da wajen kasar mamaki.

Sanarwar misis Clinton na zuwa ne a daidai lokacin da dubban Amurkawan ke ci gaba da zanga-zangar rashin amincewa da zabbaben shugaban kasar Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 45.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.