Isa ga babban shafi
Faransa

Darikar Katolika a Faransa ta nemi gafara

Shugabannin Darikar Katolika a kasar Faransa sun nemi gafarar mutanen da aka ci zarafinsu sakamakon wasu bayanan fallasar da ya nuna cewar limaman cocin sun dade suna lalata da kananan yara.

Darikar Katolika
Darikar Katolika /REUTERS/Saad Shalash
Talla

Rahotanni sun ruwaito cewar shugaban mabiya darikar da ke Lyon Archbishop Philippe Barbarin ya rufa asirin bayanan da ya samu game da limaman da suka kwashe shekaru 25 suna lalata da kananan yara.

Wannan shi ne labari mafi muni da ya shafi cocin tun shekarar 2011 lokacin da aka dakatar da wani Bishop watanni uku saboda ya ki fallasa irin wannan labari.

Rahotanni sun ce akwai sakwannin imel sama da 100 da cocin ta samu a tsawon watanni shida da ke bayani akan lalata da yara tun a 1960.

Shugaban darikar da ke Paris, Andre Vingt-Trois ya shaidawa mabiyansa cewar cocin ta gaza wajen kare yaran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.