Isa ga babban shafi
Faransa

Mahawara ta biyu na 'yan Republican a Faransa

Tsohon Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya fuskanci suka sosai kan rawar da gwamnatin sa ta taka tsakanin shekara 2007 zuwa 2012 a mahawarar da aka fafata tsakanin mutane 7 dake neman ganin Jam’iyyar su ta republican ta tsayar dan takara a zaben shekara mai zuwa.

Mahawara ta biyu daga ya'an jam'iyyar Republicain a Faransa
Mahawara ta biyu daga ya'an jam'iyyar Republicain a Faransa REUTERS/Eric Feferberg
Talla

Sauran 'yan takaran sun dauki dogon lokaci suna sukar manufofin tsohon shugaban wanda aka bari yana ta kokarin kare kan sa dama rawar siyasa da ya taka na lokacin.

Sakamakon mahawarar ya nuna cewar Alain Juppe, tsohon Firaministan Sarkozy ne ya lashe da kashi 34 daga cikin dari, yayin da tsohon shugaban yake da  kashi 24 daga cikin dari.

Faransawa na sa ran ganin jam'iyyar Republican ta dore dama samar da sabbin alkawura  na maido Faransa a sahun gaba na kasashen dake fada  a ji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.