Isa ga babban shafi
Italiya

Sabuwar girgizar kasa ta afka wa Italiya

Wata girgizar kasa mai karfin maki shida da digo shida ta afka wa yankin tsakiyar kasar Italiya, in da ta ruguza gidaje masu tarin yawa tare da raunata jama'a.

Girgizar kasar ta ruguza gidaje da dama a Italiya
Girgizar kasar ta ruguza gidaje da dama a Italiya Reuters/路透社
Talla

Kawo yanzu ba a samu labarin samun asarar rayuka ba a girgizar wadda ita ce ta uku a cikin watanni biyu, yayin da aka kwashe mutane da dama daga yankin da lamarin ya faru

Rahotanni sun ce da dama daga cikin jama’ar yankin sun kwana ne a cikin motoci da tantuna da kuma wasu wurare na wucin gadi saboda ibtila'in.

Girgizar ta auku ne a kusa da yankin da aka taba samun irin wannan ibtila’in a cikin watan Agustan da ya wuce, in da kimanin mutane 300 suka hallaka.

A halin yanzu dai dubban jama'a na ta gararamba a kan tituna, in da wasu ke ta koka saboda razanar da suka yi a sanadiyar girgizar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.