Isa ga babban shafi
Iraqi-EU

Matan kabilar Yazidi sun lashe kyautar Sakharov

Wasu mata biyu ‘Yan kabilar Yazidi a Iraqi da suka samu tsira daga yanayi na ban tsoro na fyade da bauta a hannun Mayakan IS sun lashe kyautar Sakharov ta ‘Yancin Dan Adam da Majalisar Tarayyar Turai ke bayarwa.

Nadia Murad, da ta sha wahala a hannun IS
Nadia Murad, da ta sha wahala a hannun IS REUTERS
Talla

Bayan sun tsira daga hannun IS, Nadia Murad da Lamia Haji Bashar sun kasance ‘Yan gwagwarmayar kare ‘yan kabilar Yazidi mabiya wani tsohon addini da ke da mabiya kusan rabin miliyan a arewacin Iraqi.

A watan Agustan 2014 ne mayakan IS suka sace Murad a cikin kauyensu na Kocho da ke kusa da garin Sinjar a arewacin Iraqi.

Murad da ke bikin cika shekaru 23 a yau ta ce an azabtar da ita tare da yi mata fyade.

Haji Bashar ‘yar shekaru 16 da ita ma aka sace a kauyen Kocho ta ce bada labarin yadda mayakan IS a gaban idonta ke yi wa yan uwanta ‘yan kabilar Yazidi yankan rago.

Sannan ta ce ta shafe watanni 20 tana shiga aikin bauta a matsayin baiwa kafin ta gudu amma ta fada hannun wani jami’in wata Asibiti da shi ma ya ci mutuncinta.

Saboda dai irin wanna halin na ban tsoro da tausayi da ‘yan matan biyu suka shiga ne ya sa suka lashe lashe kyautar ta Sakharov da ake bayarwa duk shekara.

Kyautar kuma ta kunshi kudi dala dubu 55.

Bayan sanar da lashe kyautar, Nadia Murad ta ce kyautar kamar yin tir da allawadai ne da miyagun ayyukan mayakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.