Isa ga babban shafi
EU

EU na shirin tsawaita kula da kan iyakokin Schengen

Kungiyar Tarayyar Turai na shirin tsawaita kula da kan iyakokin kasashen Schengen da ake shiga ba Visa har na tsawon watanni 3 a wani mataki na magance matsalar ‘Yan gudun hijira da ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen na Turai.

Bukatar tsaron kan iyakokin Schengen na tsawon watanni uku zai soma aiki daga watan Nuwamba
Bukatar tsaron kan iyakokin Schengen na tsawon watanni uku zai soma aiki daga watan Nuwamba REUTERS/Wolfgang Rattay
Talla

Hukumar Tarayyar Turai da bangaren zartarwar kungiyar kasashen na Turai ne suka bukaci ci gaba da kula da kan iyakokin kasashen Jamus da Denmark da Austria da Sweden da kuma Norway da ba ta cikin kungiya.

Kuma bukatar tsaron kan iyakokin na tsawon watanni uku da zai soma aiki daga watan Nuwamban gobe, Hakan na nufin an tsawaita wa’adin aikin tsaron kan iyakokin ne yayin da wa’adin da kasashen suka diba tun da farko zai kawo karshe a karshen shekarar nan.

Mataimakin shugaban hukumar ta Tarayyar turai Frans Timmermans ya fadi a cikin wata sanarwa cewa suna iya kokarin ganin sun dawo da tsohon tsarin Schengen da ke bada damar shiga wasu kasashen na Turai ba tare da wani shamaki ba

Hukumar ta ce akwai bakin haure da dama a Girka da sauran kasashen Turai, wanda hakan ya sa kula da kan iyakoki ya zama wajibi domin magance kwararar bakin.

Yarjejeniyar da Tarayyar turai ta kulla da Turkiya a watan Maris dai ya taimaka wajen takaita shigar 'yan gudun hijirar Syria zuwa kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.