Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya bayyana manufofin da zai aiwatar a kwanaki 100 bayan cin zabe

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin Jam’iyyar Republican Donald Trump, ya bayyana manyan abubuwan da zai aiwatar cikin kwanaki 100 na farko, muddin ya zama shugaban Amurka.

Dan takara shugabancin Amurka karkashin Republican Donald Trump
Dan takara shugabancin Amurka karkashin Republican Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Trump ya ce zai maida bakin haure sama da Miliyan biyu kasashensu, wadanda ya bayyana a matsayin miyagu, sai kuma daina biyan kudade ga Majalisar Dinkin Duniya, saboda gudunmawar da Amurka ke badawa wajen gurbata yanayi.

A gefe guda kuma bincike ya nuna cewa, Donald Trump na kara samun tagomashin magoya baya, domin kuwa a yanzu yana da goyon bayan kashi 40%, yayinda Clinton ke da 44%, sabanin a da, da Trump din ke da goyon bayan 37%.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.