Isa ga babban shafi
Italiya

Musulmi sun yi zanga zangar lumana a birnin Rome

Daruruwan Musulmi ne suka gudanar da zanga zangar lumana a birnin Rome, don nuna rashin amincewa da yadda aka rufe wasu masallatai a kasar Italiya.

Talla

A watan Agustan da ya gabata ne Ministan cikin gida na Italiya, Angelino Alfano yace gwamnatin kasar, ba zata amince da kafuwar kananan masallatai a kasar ba.

A halin yanzu, hukumar ‘yan sandan Italiya ta tabbatar da rufe masallatai dama, sai dai ta ce kowa na da damar yin ibadarsa, amma cikin tsarin dokokin kasar.

Alkalumma sun nuna cewa akalla Musulmai sama da miliyan daya ke rayuwa a kasar, kuma addinin muslunci ne na biyu mafi karbuwa a birinin Rome, sai dai da dama daga cikin Musulman na zargin hukumomin italiya da nuna musu wariya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.