Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta dakatar da matakin maida 'yan Haiti kasarsu

Gwamnatin Amurka ta jingine matakin da ta dauka na mayar da ‘yan kasar Haiti da ke zaune a kasar ba tare da takardun izinin zama ba.

Sakataren tsaron Amurka na cikin gida Jeh Johnson
Sakataren tsaron Amurka na cikin gida Jeh Johnson
Talla

Sakataren harkokin tsaron cikin gida na Amurka, Jeh Johnson, ya ce an dauki wannan mataki don tallafawa wadanda guguwar Mathew ta aukawa.

Tun da fari dai a shekara ta 2010 Amurka ta fara jingine matakinta na mayar da ‘yan Haiti da ke zaune a kasar ba bisa ka’ida ba saboda girgizar kasar da ta auka mata, da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 220,000.

Bayan samun saukin yanayin da girgizar kasar ta haifar a Haitin Amurka ta cigaba da maida ‘yan kasar da basu da takardar izinin zama.

To sai dai ganin dubban ‘yan Haitin da suka kwarara zuwa garin Tijuana ke kan iyakar Amurka da Mexico ya sa gwamnatin Obama sanar dakatar da cigaba da mayar da ‘yan Haitin kasarsu.

Sakataren harkokin tsaron cikin gida na Amurka Jeh Johnson y ace tilas a taimakawa, “yan Haitin masu neman shiga Amurka da nufin samun kulawa bayan fuskantar bala’in guguwar Mathew.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.