Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka zata taimaki Turkiya hukunta masu hannu cikin yunkurin juyin mulki

Shugaban Amurka Barrack Obama ya ce gwamnatinsa zata taimakawa Turkiya wajen ganin an tabbatar da hukunci kan duk wanda aka samu da hannu a kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar.

Shugaban Amurka Barack Obama yayin daya sauka a filin jiragen sama na Hangzhou Xiaoshan da ke China
Shugaban Amurka Barack Obama yayin daya sauka a filin jiragen sama na Hangzhou Xiaoshan da ke China Reuters/路透社
Talla

Obama ya bayyana hakan a taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na G20 kashi na 11 da yake gudana a Hangzhou da ke China.

Tun a watan Yulin da ya gabata, Turkiya ta zargi fitaccen malamin addinin kasar da ke zaune a Amurka Fethullah Gulen da shirya juyin mulkin.

A watan da ya gabata gwamnatin Turkiya ta bukaci Amurka ta mika mata Gulen, yayin da Amurkan ta ce zata yi hakan amma bisa sharadin sai Turkiyan ta gabatar da shaidun da zasu tabbatar da zargin da ake yiwa Gulen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.