Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da matakin kotun kolin Faransa
Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da matakin da kotun kolin kasar Faransa ta dauka na watsi da dokar sanya kayan matar da ya haifar da zazzafar mahawar a kasar, inda take cewa matakin ya haifar da tsangwamar addini.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yauwn hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar Rupert Colville, yace irin wannan mataki da wasu garuruwan Faransa suka dauka baya samar da tsaro sai dai haifar da tsangwamar addini musamman ga mata Musulmai da ke kasar.
Majalisar tace irin wannan doka na shafar mata wajen tauye musu hakkokin su da kuma hana su zabin irin kayan da suke so su saka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu