Isa ga babban shafi
Bolivia

Masu zanga zanga sun kashe Mataimakin Minista

Shugaban kasar Bolivia Evo Morales ya alakanta kashe mataimakin Ministan cikin gidan kasar, da wasu masu hakar ma’adanai da ke zanga zanga suka yi, da cewa tuggun siyasa ne da ‘yan adawa ke kullawa gwamnatinsa. 

Gwamnatin Bolivia tana alhini kashe Rodolfo Illanes
Gwamnatin Bolivia tana alhini kashe Rodolfo Illanes REUTERS/Bolivian Presidency
Talla

Mataimakin Ministan Rodolfo Illanes ya rasa ransa ne bayan sace shi da mahaka ma’adanan da ke zanga zanga suka yi, tare da zabtar da shi ta hanyar yi masa dukan kawo wuka, a lokacin da ya yi yunkurin tattaunawar sulhu da su.

Yayin da yake Ala wadai da kisan a gidan talabijin na kasar, Ministan tsaron Bolivia Reymi Ferreira ya barke da kuka lokacin da yake bayanin yanayin da Illanes ya shiga kafin rasa ransa, a garin Panduro da ke yammacin Bolivian.

Kisan ya girgiza mutanen kasar musamman shugaban Bolivian Morales wanda yake ganin yana kyakkyawar alaka tsakaninsa da kungiyoyin kwadago a kasar.

Morales ya zargi masu adawa da gwamnatinsa wajen amfani da jerin zanga zangar da kungiyoyin sufuri da masu hakar ma’adanai ke yi wajen haifarwa da gwamnatinsa matsaloli.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.