Isa ga babban shafi
Argentina

Kotu ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan mutane 28

Wata kotu a kasar Argentina ta zartar da hukuncin daurin rai da rai akan mutane 28, wadanda ake zargin sun azabtar da mutane tare da murkushe ‘yan adawa a zamanin mulkin Sojoji na kama-karya tsakanin 1976 zuwa 1983.

Shugaban kasar Argentina Mauricio Macri.
Shugaban kasar Argentina Mauricio Macri. REUTERS/Agustin Marcarian
Talla

Cikin mutane 28 da kotun ta zartarwa hukuncin akwai toshon janar din sojan Luciano Menendex da ake wa kirari da kura.

Menendez mai shekaru 89 ana tuhumar sa da laifukan kisa har 52 da wasu laifukan da suka shafi garkuwa da mutane da azabtarwa tare da laifin kwace jarirai sama da 700.

Sannan kotun ta argentina ta zartar da hukuncin daurin shekaru 21 akan wasu mutanen 10.

Sama da mutane dubu talatin aka kashe a lokacin mulkin na su Menendez tsakanin shekarar 1976 zuwa 1983.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.