Isa ga babban shafi
Faransa

Ana rububbin Kayan wankan mata da faransa ta hana sawa

Kamfanin dake saka kayan da mata ke sanyawa dan wanka a bakin teku da hukumomin kasar Faransa suka haramta sanyawa yace ya samu gagarumar kasuwa wajen yadda ake kokawar sayen kayan daga matan da ba Musulmai ba.

Faransa ta hana mata sanya Burqa a bakin Ruwa
Faransa ta hana mata sanya Burqa a bakin Ruwa
Talla

Hukumomin Faransa sun hana amfani da kayan dake rufe jikin mace baki daya a garuruwa 15 saboda abinda suka kira saba al’adun mutanen kasar.

Sai dai kamfanin dake Australia yace takaddamar ta Faransa ya sa kayan ya samu kasuwa sosai.

Shugabar kamfanin Aheda Zanetti tace a ranar lahadi kawai sun samu oda 60 na masu bukatar kayan kuma dukkan su sun fito ne daga wadanda ba Musulmai ba.

Batun sanya irin wanna kaya da ake kira Burkini ya haifar da rarrabuwar kawuna a kasar ta Faransa bayan kotu ta ki amincewa da daukaka karar.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.