Isa ga babban shafi
Czech

Jamhuriyyar Czech na kyamar Musulmi 'Yan gudun hijira

Firaministan Jamhuriyar Czech ya ce bai yarda a bai wa bakin-haure musamman musulmi damar zama a cikin kasarsa ba, karkashin tsarin Tarayyar Turai na raba yawan ‘Yan gudun hijira tsakanin kasashen Nahiyar.

Firaministan Jamhuriyyar Czech Bohuslav Sobotka
Firaministan Jamhuriyyar Czech Bohuslav Sobotka © Reuters/David W Cerny
Talla

Firaminista Bohuslav Sobotka, ya ce yana adawa da bai wa musulmi damar kwarara a Czech saboda matsalolin da suke gani na faruwa a wasu kasashe.

Ya ce gwamnatin shi za ta ci gaba da sa-ido domin tabbatar da hakan ba ta faru ba.

Mista Sobotka ya fadi matsayin kasarsa ne kafin ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da za ta kawo ziyara a Prague domin tattauna matsalar ‘Yan gudun hijira.

Jamhuriyyar Czech dai na adawa da tsarin Tarayyar Turai na rarraba ‘Yan gudun hijira tsakanin kasashen nahiyar.

Firaministan ya ce ya dace a yi la’akari da yawan ‘Yan gudun hijirar da kasashen ke iya karba da kuma yanayinsu.

Tuni dai shugaban kasar Milos Zeman ya ce kasar shi ba za ta karbi dan gudun hijira ko guda ba.

Wasu kasashen Turai dai na dora laifin hare haren ta'addanci da ke faruwa a wasu kasashe akan 'Yan gudun hijira wadanda ke kwarara domin neman mafaka daga yakin Syria da Iraqi da rikicin Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.