Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy zai tsaya takarar zaben 2017 a Faransa

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar zaben shugaban kasa da za a gudanar a 2017. Sarkozy ya sanar da aniyarsa ne a cikin wani littafin da ya rubuta wanda za a kaddamar a ranar Laraba.

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy Benoit Tessier/Reuters
Talla

Sarkozy wanda ya shugabanci Faransa a 2007 zuwa 2012 ya bayyana manyan kalubale guda biyar da zai tunkara idan har ya sake cin zaben shugaban kasa.

Sarkozy zai tsaya takara ne karkashin jam’iyyar shi ta Republican.

Francois Hollande ne ya kayar da Nicolas Sarkozy a zaben 2012, kuma yanzu ana hasashen yana iya doke Hollande a zaben 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.