Isa ga babban shafi
Philippines

Duterte yayi barazanar fitar da kasar daga cikin MDD

Shugaba Rodrigo Duterte yayi barazanar fitar da kasar daga cikin Majalisar Dinkin Duniya sakamakon sukar da ta yi masa kan yadda yake kashe wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ba tare da an kaisu gaban kotu ba.

Shugaba  Rodrigo Duterte ya sha alwashin magance matsalar safarar miyagun kwayoyi a kasar
Shugaba Rodrigo Duterte ya sha alwashin magance matsalar safarar miyagun kwayoyi a kasar REUTERS/Noel Celis/Pool/File Photo
Talla

Shugaba Rodrigo Duterte wanda yayi alkawarin magance matsalar safarar kwayoyi da suka addabi kasar, ya baiwa Yan Sanda umurnin harbe duk wani mutumi da ake zargi da mu’amala da kwayoyin wanda yaki mika kan sa.

Duterte ya bukaci manyan jami’an soji da Yan Sanda tare da alkalai da ake zargin suna da hannu wajen safarar kwayoyin da su kai kan su ofishin Yan Sanda ko kuma a harbe su nan take.

Wannan ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwar ta ganin yadda ake taka hakkin Bil Adama a kasar, abinda bai yiwa shugaban dadi ba, inda ya bayyana shirin ficewar kasar daga Majalisar.

Shugaba ya bayyana Majalisar a matsayin kyanwan yaya lami wadda ta kasa kawo karshen kisan gillar da akeyi a Gabas ta Tsakiya da kuma halin da ake ciki a Afirka, Syria da Iraqi.

Duterte yayi misali da karamin yaron da ya tsira daga harin Syria akan yadda Majalisar ta gaza wajen cewa uffan akai.

Akalla mutane 1,500 aka kasha yanzu haka a Philippines.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.