Putin ya kai ziyara yankin Crimea
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kai ziyara yankin Crimea, kwana guda bayan ya zargi Ukraine da kokarin mamaye yankin.
Wallafawa ranar:
Wannan dai wata sabuwar barazana ce ta kunno kai tsakanin Ukraine da Rasha kan yankin na Crmea.
Wannan shine karo na biyar da Putin ke kai ziyara a Crimea bayan yankin ya balle daga Ukraine a watan Maris na 2014.
Shugaba Putin zai gana da babbar majalisar tsaro ta yankin na Crimea tare da kai ziyara wajen wani taro na matasa da za’a gudanar.
A watan jiya ne Rasha ta zargi Ukraine da tura wasu dakarunta a Crimea da nufin dagula zaben da ake shirin yi a yankin.
Jami’an tsaron Rasha biyu aka kashe a harin amma Ukraine musanta zargin na Rasha.
Tun 2014 Ukraine ke fada da ‘yan a ware a gabashin kasar wadanda ke ra’ayin Rasha sabanin Ukraine da ke ra’ayin Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu