'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a cocin Faransa
Wani limamin cocin Faransa ya rasa ransa bayan wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da jama’a a cikin cocin wanda ke kusa da birnin Rouen na arewacin kasar.
Wallafawa ranar:
‘Yan bindigar sun kutsa cikin cocin ne a lokacin da ake gudanar da bauta, inda suka yi garkuwa da limamin da wasu daga cikin masu ibada.
Kafofin yada labaran Faransa sun rawaito cewa, an jin karar harbe -harben bindiga bayan jami’an tsaro sun isa wurin, inda suka kashe ‘yan bindigar guda biyu.
Tuni dai aka killace wurin da lamarin ya faru yayin da hukumomi suka bukaci jama’a da su kauracewa wurin.
Shugaban Faransa Francois Hollande da ministan cikin gida Bernard Cazeneuve na kan hanyarsu ta zuwa birnin na Rouen don sanin halin da ake ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu