Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta karrama Australia da New Zealand

Faransa za ta karrama kasashen Australia da kuma New Zeland a bikin ranar ‘yancin kasar na bana da za a yi a ranar 14 ga wannan wata na Yuli saboda rawar da suka taka a yakin duniya na farko wajen kare Faransa.

Wasu dakaru da suka fafata a fadan Somme wanda aka yi a yakin duniya na farko a ranar 1 ga watan Yulin shekara ta 1916 1916.
Wasu dakaru da suka fafata a fadan Somme wanda aka yi a yakin duniya na farko a ranar 1 ga watan Yulin shekara ta 1916 1916. Getty Images/The Print Collector
Talla

A wurin bikin tunawa da zagayowar ranar juyin-juya halin Faransa da ake kira da ranar bikin Bastille, an gayyaci mutane 150 daga Australia da kuma wasu 85 daga kasar New Zeland domin shiga faretin soji da za a yi a harabar fadar shugaban kasar ta Elysees da ke Paris.

Wannan dai na a matsayin karamci ga kasashen biyu, wadanda suka taka gagarumar rawa a fadan da aka gwabza a Somme shekarar 1916 lokacin yakin Duniya na daya.

Kasashen biyu sun rasa sojoji akalla dubu 30 a lokacin wannan fada.

Bikin zagayowar ranar juyin-juya halin Faransa a bana, ya zo ne a daidai lokacin da Faransa ta samu kwangilar kera wa Australia jiragen yaki na karkashi teku 12 a kan dala bilyan 39.

A faretin bikin da za a yi a bana, akwai sojoji da ‘yan sanda da kuma jandarma har dubu 3 da 239 daga Faransa da kuma wasu kasashe da aka gayyata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.