Isa ga babban shafi
Turai- Birtaniya

Turai ta ci gaba da taro ba tare da Birtaniya ba

Shugabannin kasashen Turai za su ci gaba da gudanar da taronsu a birnin Brussels ba tare da Birtaniya ba wadda ta fice daga Turai bayan ta kada kuri’ar raba gardama a makon jiya.

Firaministan Birtaniya David Cameron da shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker a birnin Brussels na kasar Belgium.
Firaministan Birtaniya David Cameron da shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker a birnin Brussels na kasar Belgium. REUTERS/ Francois Lenoir
Talla

A jiya Talata ne Firaministan Birtaniya, David Cameron ya shaida wa shugabannin Turai 27 cewa, ci ga da huldar kasuwanci da tsaro a tsakaninsu na da matukar muhimmanci.

Sai dai Mr. Cameron ya zargi manufofin karbar baki a matsayin abinda ya tinzira ‘yan kasar har suka zabi raba gari da kungiyar tarayyar Turai, yayin da shugabannin kungiyar ke cewa ba za su tattauna da Birtaniya ba har sai ta gabatar da matsayinta kan wannan batu a hukumance.

Shugabar gwamnatin Jamsus, Angela Mrekel ta bukaci kungiyar da ta mutunta sakamakon zaben na raba gardamar yayin da ake saran kammala taron a yau.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.