Isa ga babban shafi
Belgium

Belgium ta cafke mutane 6 kan harin ta’addanci

‘Yan Sanda a kasar Belguim sun sanar da kama mutane 6 da ake zargin suna da hannun wajen yunkurin kai hari tashar jirgin kasa da ke tashi daga Amsterdam zuwa Brussels da Paris.

Belgium ta cafke dan uwan Mohammed Abrini
Belgium ta cafke dan uwan Mohammed Abrini
Talla

Cikin wadanda aka cafke sun hada da dan uwan Mohammed Abrini wanda ake zargi cikin wadanda suka kai hari a Paris.

Ofishin mai gabatar da kara na kasar ya ce an gurfanar da mutanen shida a gaban kotu domin tuhumarsu duk da ya ke babu wanda aka samu da makami ko bam tare da su.

Kasar Belguim na daya daga cikin kasashen da suka fuskanci harin ta’addanci a kasashen Turai, bayan kai mummunan harin da aka kai a Paris a ranar 13 ga watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.