Isa ga babban shafi
TARAYYAR TURAI-BAKIN-HAURE

An tsinto jinjira a tsibirin Lampedusa

An ceto wata jinjira ‘yar watanni 9 a duniya a tsibirin Lampedusa, na kasar Italiya, a jiya laraba ne dai jami’an tsaron gabar ruwan na kasar Italiya suka ceto jinijirar a matsayi marainiya, bayan da iyayenta suka mutu a lokacin da kwale kwalen da suke ciki ya kife a teku.

Wasu daga cikin Bakin haure dake kokarin tsallaka wa turai
Wasu daga cikin Bakin haure dake kokarin tsallaka wa turai EUNAVFOR MED
Talla

A cikin yanayi na alhini a gaban ‘yan jaridu, Dakta Pietro Bartolo, likita guda daya tilo dake aiki a tsibirin na Lampedusa, ya bukaci mahukuntan kasar su barmasa jijirara ya reneta a matsayi diya.

An dai bayyana cewa, iyayen ita wannan jinjira ‘yan kasar Mali ne, kuma dukkaninsu sun mutu a hadarin jirgin ruwan dake dauke da bakin haure 120 ‘yan akasarinsu ‘yan kasashen Mali da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.