Isa ga babban shafi
Faransa

Yajin aikin Faransa ya yi illa ga gidajen mai

Kungiyoyin CGT da FO sun kira wani yajin aiki a dukkanin fadin Faransa domin nuna adawa da shirin gwamnati na samar da sauye sauye a dokar kwdago ta kasar, abinda ya haifar da rashin mai a wasu gidajen mai.

Jami'an 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a Marseille
Jami'an 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a Marseille BORIS HORVAT / AFP
Talla

Yajin aikin ya shafi daukacin matatun man fetir guda takwas da ke kasar yayin da kashi 20 cikin 100 na gidajen mai suka tsindima cikin matsalar rashin mai.

Wata tarzoma da ta barke a matatar mai ta Fos-sur –Mer da ke kudancin Marseille, inda jami’an 'yan sanda suka tarwatsa masu zanga zanga tare da yin fatali da karikitan da suka yi amfani da su wajen rufe hanya.

Ministan sufurin kasar Alain Vidalies ya bayyana cewa, kimanin gidajen mai dubu 1 da 500 daga cikin dubu 12 da ake da su a Faransa na cikin matsalar rashin mai.

Shi kuwa Firaministan kasar Manuel Valls cewa ya yi, gwamnati za ta tabbatar da wannan dokar duk da zanga zangar da ake yi, kuma jami’an 'yan sanda za su ci gaba da tarwatsa gangamin masu zanza zangar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.