An kaddamar da farmaki akan mayakan ISIL a Syria da Iraki
Masu sa ido a rikicin Syria sun ce mayakan ISIL na amfani da mutane a matsayin garkuwar yaki a yayin da ake masu luguden wuta a yankin Raqa, a yayin da dakarun kawancen kasashen larabawa dana kurdawa suka kaddamar da farmaki akan mayakan na ISIL a Syria da Iraki.
Wallafawa ranar:
Dakarun kawancen na kasashen Larabawa da na kurdawaa sun farwa mayakan ISIL a yankin Raqa na Syria a yayin da kuma dakarun Iraki suka doshi yankin Fallujah domin fattakar mayakan.
Masu sa ido a rikicin na Syria sun ce mayakan na amfani da fararen hula a matsayin garkuwar yaki.
Wani dan Raqa kuma mai fafutika Abdel Aziz al Hamza wanda ya gudu zuwa Jamus yace mayakan na fakewa a gidajen fararen hula da makarantu domin tsira daga luguden wutar da ake yi masu da jiragen yaki.
Dubban mutane aka ruwaito an yiwa kawanya a yankin Raqa kuma babu yadda zasu iya ficewa daga yankin saboda yaki.
Kungiyar da ke sa ido a rikicin Syria tace mayakan ISIL kimanin 22 aka kashe a hare haren sama da aka kai wa mayakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu