Isa ga babban shafi
Austria

Ana dakon sakamakon zaben Austria

‘Yan takara biyu da suka kara a zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar Austria da aka gudanar a jiya lahadi, Norbert Hofer da kuma Alexander Van der Bellen, sun yi kafada da kafada ta fannin yawan kuri’u. 

Alexander Van der Bellen da Norbet Hofer da ke nema kujerar shugaban kasar Austria
Alexander Van der Bellen da Norbet Hofer da ke nema kujerar shugaban kasar Austria REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

Wani lokaci a yau ne ake kyautata zaton cewa za a fitar da sakamakon zaben, bayan kammala kirga kuri’un da aka jefa a kasashen ketare

Yanzu haka dai hankulan jama’a a kasar da ma sauran kasashen yankin Turai sun karkata ne zuwa ga kasar domin sanin wanda zai jagoranci kafa gwmanati tsakanin Hofer mai ra’ayin rikau da kuma Alexander na jam’iyyar masu ra’ayin kare muhalli.

Alkalumman da aka fitar zuwa yammacin jiya na nuni da cewa mutanen biyu na gogayya ne da juna ta fannin kuri’u, duk da cewa da farko an yi hasashen dan takarar na masu ra’ayin rikau, wanda kuma sau da dama yana fitowa fili domin nuna kyamar baki ne zai yi nasara ba tare da wata matsala ba.

A zagayen farko na zaben da aka gudanar ranar 24 ga watan Afrilun da ya gabata, karo na farko a tarihi wadannan jam’iyyun biyu sun yi nasarar zuwa zagaye na biyu a cikin shekaru sama da 60.

Matukar dai dan takarar jam’iyyar ta masu ra’ayin rikau Norbert Hofer ya lashe wannan zabe, to hakan zai kasance babban abin farin ciki ga Marine Le Pen da ke da irin wannan ra’ayi sannan kuma take shirin tsayawa takara a zaben shugabancin Faransa a shekara mai zuwa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.