Isa ga babban shafi
Faransa

Daurin shekaru 8 akan likitan da ya cire hakoran marasa lafiya

Kotu ta yanke hukuncin dauri na shekaru 8 kan wani likitan haure dan asalin kasar Netherland bayan ya aikata laifin cirewa marasa lafiya hakora a yanayin da bai dace ba.

Zanen likitan Mark Van Nierop
Zanen likitan Mark Van Nierop AFP/Benoit Peyrucq
Talla

Ana dai zargin likitan hakoran ne mai suna Mark Van Nierop da cutar da wadanda yake kula da su ne tsakanin shekara ta 2008-2012, inda mutane sama da 100 daya suka shigar da kararsa a gaban kotu.

Kotun dai ta amince ta saurari kararraki 53 daga cikin mutanen da ke zargin likitan da cire masu hakora ko kuma ji masu rauni da gangan, yayin da kotun ta yi watsi da sauran zarge-zargen da ake yi masa.

Lokacin da aka fara zarginsa da raunata jama’a, sai likitan ya rufe asibitinsa sannan ya ce yana fama da matsalar shanyewar hannu, kuma daga nan sai ya gudu zuwa kasar Canada kafin a taso keyarsa zuwa Faransa a shekara ta 2014.

Babban abin da kotun ba ta bayyana a wannan hukunci ba, shi ne Dr Mark Van Nierop ya rika raba jama’a da hakoransu ne da gangan ko kuma saboda rashin kwarewa akan aikinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.