Isa ga babban shafi
EU

EU zata gurfanar da kamfanin Google don tallata wayar android a Yankin.

A gobe laraba ne ake saran kungiyar kasashen Turai zata gurfanar da kamfanin Google saboda yadda ya tallata wayar salularsa ta android a Yankin.

Kanfanin Google
Kanfanin Google RFI/Thomas Bourdeau
Talla

Wannan kara da kungiyar kasashen Turai zata gabatar zai zama babbar koma baya ga kamfanin na Google mallakar kasar Amurka, wanda ake zargi da karya doka wajen tallata wayarsa ta android.

Tuhumar na zuwa ne bayan karar da akayi kan yadda kamfanin Google ke gudanar da cinikayyarsa a shekarar da ta gabata.

Kwamishiniyar kungiyar kasashen Turai Margereth Vestager ake sa ran zata bayyana tuhume tuhumen da ake yiwa katafaren kamfanin da suka hada da yadda yake fifita tallata na’urar sa da suka kunshi zanen kasa da kuma wakoki a kwangilar da ya kulla da kamfanoni irin su Samsung da Huawei.

Shi dai kamfanin na android ke da kashe 80 na kasuwanin na wayoyin salula a duniya, wanda ya nuna cewar ya yiwa kamfanin Apple fintinkau.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.