Isa ga babban shafi
Girka

EU ta ba Girka wa’adi kan ‘Yan gudun hijira

Kungiyar Tarayyar Turai ta ba Girka nan da ranar 26 ga watan Afrilu da ta fayyace shirinta na tsare kan iyakatarta saboda kwararar ‘yan gudun hijira, ko kuma ta fuskaci barazanar dakatar da ita daga amfani da tsarin biza na bai daya ta Schengen.

Girka na mayar da 'Yan gudun hijira a Turkiya
Girka na mayar da 'Yan gudun hijira a Turkiya REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

Tarayyar Turai na a aiwatar da shirin domin Girka ta gyara matsalolin da aka samu a watan Janairun da ya gabata wajen yi wa daruruwan dubban ‘yan gudun hjirar da suka fito daga Turkiya rajista tare da daukan hoton yatsunsu.

Ana sa ran Girkan ta yi wannan gyaran a tsakiyar watan Mayu mai zuwa yayin da hukumar r Turai ta caccaki shirin Girka na farko wanda ya nuna matsalolin da aka samu .

Yanzu haka dai ya zama wajibi ga mahukuntan Athens su bayyana hukumomin da za su aiwatar da sabon shirin da kuma yadda zai lakume kudaden da Tarayyar Turai ta ware domin tsare kan iyakar saboda kwararar bakin haure.

A sanarwa da ta fitar, Tarayyar Turai ta ce, matukar Girka ta gaza magance matsalolin da aka samu a baya nan da ranar 12 ga watan Mayu, lallai za ta umarci sauran mambobinta da su tsawaita tsare kan iyakokinsu har na tsawon shekaru biyu a maimakwan watanni shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.