Isa ga babban shafi
EU

EU Za Ta Tilastawa Manyan Kamfanonin Bayyanan Dukiya Da Suka Mallaka a Turai

Kungiyar Tarayyar Turai, ta kaddamar da wani sabon tsari domin tilastawa manyan kamfanonin duniya dake kasashen su su rika gabatar da cikakken bayani gameda dukiyar da suka mallaka da biyan haraji ganin irin abin fallasan da aka bankado a Panama.

Tambarin kungiyar Tarayyar Turai
Tambarin kungiyar Tarayyar Turai Union Européenne
Talla

Hukumar kasashen Turai ta fadi yayin kaddamar da wannan sabon tsari cewa manyan kamfanoni dake Turai ya zama jazamal, su rika gabatar da irin dukiyar da suka mallaka a kowace kasa daga cikin kasashen kungiyar  28.

Masu rajin ganin ana biyan haraji sun sha bukatar ganin manyan kamfanoni na biyan harajin, inda har suke zargin cewa manyan kamfanonin kan rika wata dabara wajen jibge dukiyar da suka mallaka a kasashen da basa karban haraji mai kauri, kamar  yadda tonon sililin  Panama.

Jonathan Hill Kwamishinan harkokin kudade na kungiyar tarayyar Turai ya shaidawa manema labarai a Strasbourg na kasar Faransa cewa tonon sililin da akayi na Panama,  bama shine ya zaburar dasu ba, amma suna da burin ganin ba'a wasa da batun biyan kudaden haraji.

A cewar Hukumar kasashen Turai kauracewa biyan haraji kan sa kasashen turai hasarar kudade da suka kai tsakanin biliyan 50 zuwa 70 duk shekara
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.