Isa ga babban shafi
Bosnia

Bosnia: Alhamis za a yanke wa Saselj hukunci

A ranar Alhamis ne ake sa ran kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya da ke birnin Hague za ta yanke hukunci kan tuhumar da ake yi wa daya daga cikin shugabanin Sabiyan Bosnia Vojislav Seselj.

Kwamandan Sabiyan Bosnia Vojislav Seselj
Kwamandan Sabiyan Bosnia Vojislav Seselj REUTERS/Marko Djurica
Talla

Mako guda bayan daure shugaban Sabiyawa Bosniya Radovan Karadzic shekaru 40 a gidan yari bayan samun shi da laifin kisan kare dangi, a ranar Alhamis ne kuma Alkalan kotun duniya za su yanke hukunci kan wani shugaban Sabiyawan Vojislav Seselj wanda shi ma ke fuskantar tuhumar laifufukan yaki.

Wannan shi ne karo na farko da alkalan kotun zasu yanke hukunci ba tare da wanda ake zargi na cikin kotun ba, saboda damar da kotun ta bai wa wanda ake zargin na kula da lafiyar shi.

Kotun ta bai wa Seselj damar komawa Sabiya a shekarar 2014 domin jinyar cutar kansar da ya ke fama da ita, duk da ya ke sun ce rashin lafiyar ba zai hana ci gaba da shari’ar ba.

Ana dai tuhumarsa ne da laifufukan da suka kun shi kisa, azabtarwa, cin zarafi, korar jama’a da kuma lalata wuraren ibada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.