Isa ga babban shafi
Bosnia

Daurin shekaru 40 akan Jagoran Sabiyawa Karadzic

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta Duniya dake Hague ta zartas da hukuncin zaman gidan yari na shekaru 40 akan tsohon jagoran Serbiyawa Radovan Karadzic bisa hannu a laifukan da suka kunshi kisan kiyashi dana yaki a yayin yakin kasar Bosnia da Yugoslavia

Radovan Karadzic a gaban kotun Hague
Radovan Karadzic a gaban kotun Hague Reuters / Michael Kooren
Talla

Alkalan kotun dake shari’ar karar sun sami Radovan Karadzic da hannu acikin laifuka goma cikin goma sha daya da aka shigar a gaban kotun inda daga karshe kotun ta zartas da hukuncin zaman gidan yari na shekaru 40 akan tsohon jagoran Sabiyawan

Babban alkalin kotun O-Gon Kwon yace Radovan Karadzic yana da hannun a kisan kiyashi tare da tilastawa al’umma barin gidajensu a wannan yakin

Karadzic zai sake fuskantar shari’a bisa wasu laifuka da suka kunshi laifukan kisan kiyashi da aka yiwa wasu musulmai 8,000 a shekara 1995 a wani yanki na Srebrenica

Mutane sama da dari daya da suka tsira daga yakin sun hada gangami dauke da alluna a wajen ginin babban kotun dake cewa muna sane da mutane sama da 8,000 da suka rasa rayukansu

Da dama daga cikin mutanen sun nuna rashin gamsuwa game da yadda kotun ta wanke Karadzic daga laifin hannu a kisan kare dangi a shekara 1995 a wasu yankunan Srebrenica 7

Radovan Karadzic mai shekaru 70 dai ya aikata laifukan yaki da aka kwatanta da munmunar yakin duniya na 2 kuma ya kasance daya daga cikin manyan shugabanin yankin Balkans da ya taba gurfana tare da fuskantar hukunci a gaban kotun Hague bisa laifin hannun a yakin Bosnia na sama da shekaru 20 da mutane akalla 100,000 suka rasa rayukansu

Karadzic dai na ci gaba da musanta tarin zarge zargen da ake yi mishi inda ya lankaya laifin kisan kiyashin akan wasu daban da yace makiyan Sabiyawa ne

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.