Isa ga babban shafi
Girka

EU za ta tallafa wa Girka akan 'yan gudun hijira

Kungiyar kasashen Turai ta EU ta bayyana wani shirin tallafa wa kasar Girka da wasu kasashen da ke fama da matsalar baki da euro miliyan 700.

Dubban 'yan gudun hijira ke cikin wani hali akan iyakar Macedonia da Girka.
Dubban 'yan gudun hijira ke cikin wani hali akan iyakar Macedonia da Girka. REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da majalisar dinkin duniya ke gargadi kan halin da dubban bakin suka shiga a iyakar kasar Macedonia da Girka.

Wannan tallafi da ke zuwa daga kungiyar ya biyo bayan korafin da kasar Girka ta yi, ganin yadda dubban bakin ke kwarara zuwa kasar.

Akalla baki miliyan guda da dubu dari daya suka rasa ta Girka zuwa Turai tun lokacin da aka samu barkewar matsalar a shekarar da ta gabata.

Kwamishinan jin kai na kungiyar kasashen Turai Christos Stylianides ya ce za a bada wadanan kudade ne a cikin shekaru uku masu zuwa, amma kashin farko na kudin da ya kai euro miliyan 325 za a mika wa Girka ne a cikin wannan shekara.

Jami’in ya ce idan shugabanin kasashen Turai sun amince, za a dinga bai wa Girka euro miliyan 200 kowace shekara.

Ita dai Girka ta bukaci a ba ta euro miliyan 520 dan daukar nauyin bakin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.