Hadarin jirgi: Gwamnatin Jamus ta kaddamar da bincike
Gwamnatin Jamus ta kaddamar da bincike kan yadda jiragen fasinjan kasar guda biyu da ke amfani da birki na musamman suka yi taho mu gama, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10, yayin da wasu da dama suka samu rauni.
Wallafawa ranar:
'Yan sandan kasar sun tabbatar da mutuwar mutanen 10, tare da fadin cewa mutane 18 sun samu rauni matuka, yayin da wasu 63 suka samu rauni masu sassauci.
Shugabar gwamnatin kasar Angela merkel ta bayyana kaduwarta da hadarin jiragen na kasa.
A shekara ta 2011 ne Jamus ta dauki wasu matakan kariya ta hanyar dasa wasu na’urori da aka fi sani da PZB 90 da ke iya daidaita birkin jirgin kasa muddun ya yi kuskuren sakin hanya, sai dai ga dukkan alamu tsarin bai yi tasiri ba ganin munin hadarin na jiya da ya jefa kasar cikin jimami.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu