Isa ga babban shafi
China

An sami bullar cutar Zika a Chana

An samu bullar cutar zazzabin Zika a kasar Chana a karo na farko, an tabbatar da hakan ne bayan an  sami wani mutum guda da ya shigo kasar daga kasar Venezuela da kwayar cutar da aka tabbatar Zika ce bayan an gudanar da gwaji a kan mutumin

Sauro ke yada kwayar cutar zika
Sauro ke yada kwayar cutar zika REUTERS/Jaime Saldarriaga
Talla

Mutumin dai na dauke da alamomin cutar da suka hada da zazzabi da ciwon kai da kuma rashin kasala, kuma bayan gwajin ne aka tabbatar cewar cutar Zika ce, al'amarin da yanzu haka ya haifar da tsoro a tsakanin al’ummar kasar dake da yawan gaske .

Ana dai danganata cutar Zika da yawan haihuwar yara masu kananan kai ko nakasu yawanci a kasashen Latin Amurka abinda yasa aka shawarci mata yanzu da su sa tazara a haihuwa akalla na tsawon shekaru biyu har sai an yi nasarar hana yaduwar cutar dama kawo karshen annobar baki daya a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.