Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Faransa ta amince da bukatun tsaurara tsaro

Karamar Majalisar dokokin Faransa ta jefa kuriar amincewa da kafa dokar ta-baci cikin kundin tsarin mulkin kasar, daya daga cikin batutuwa da ake ta tafka muhawara akai tun bayan harin ta’adanci a birnin Paris a cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Charles Platiau
Talla

Wakilai 103 suka amince da wannan bukatar yayin da wakilai 26 suka ki amincewa.

Wannan amincewa na daga cikin jerin sauye-sauyen da gwamnati ke son dauka domin yakar ta’addanci a kundin tsarin mulkin kasar

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ayyana kafa dokar ta-baci sakamakon harin ta’addanci da aka kai wani gidan rawa da ke Paris inda mutane 130 suka mutu.

Gwamnatin gurguzuu ta Hollande na son ganin an kafa wannan doka ne kamar yadda aka yi lokacin yakin kasar Algeria a shekara ta 1955.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.