Isa ga babban shafi
Jamus

Hadarin jiragen kasa ya hallaka mutane 9 a Jamus

Al’ummar kasar Jamus na jimamin mutuwar mutane 9 bayan taho mugama da jiragen kasa biyu suka yi a yau talata,Tuni  Shugabar gwamnatin Jamus Angel Merkel ta meka sakon ta’azziya ga iyalan wadanda suka rasa yan’uwa a hadarin.

Jiragen kasa biyu da suka yi karo da juna a Jamus
Jiragen kasa biyu da suka yi karo da juna a Jamus AFP
Talla

Hadarin na yau da ya matukar girgiza al’umma kasar ya auku sakamakon taho mu gama da wasu jiragen kasa biyu suka yi a yankin kudancin kasar inda nan take mutane 9 suka mutu yayin da aka kwashi wasu sama da 100 daya da suka galabaita
Yayin da masu aikin gaggawa ke cigaba da aikin ceto raguwar fasinjojin dake makale a cikin jiragen biyu.

Ministan sufurin kasar Alexander Dobrindt ya ce sun soma gudanar da bincike don gano musababin hadarin inda yace yana da wuya yanzu a tabbatar ko hadarin ya auku ne sakamakon kuskuren matukan jiragen kokuma tangardar na’ura

A shekara ta 2011 Jamus ta dauki wasu matakan kariya ta hanyar dasa wasu na’urori da aka fi sani da PZB 90 da ke iya daidaita birkin jirgin kasa muddun ya yi kuskuren sakin hanya, Sai dai ga dukkan alamu tsarin bai yi tasiri ba ganin munin hadarin na yau da ya jefa kasar cikin jimami

Yanzu dai an yi nasarar futar da bakin akwatin nan dake nadan bayanai biyu daga cikin tarkacen jirgin yayin da ake cigaba da laluben na 3, duk zasu taimaka a binciken musababbin hadarin da ya kasance mafi muni a kasar tun bayan wanda ya auku a watan afrilun 2012 da ya hallaka mutane 3 a birnin Offenbach.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.