Isa ga babban shafi
Faransa-ISIS

Muhawara kan sabon shirin yaki da ta’addanci a Faransa

A yau Juma’a Majalisar dokokin Faransa za ta fara muhawara kan daftarin da ke neman amincewa da sabbin sauye sauye na yaki da ta’addaci a kundin tsarin mulkin kasar.

Zauran Majalisar Dokokin Faransa
Zauran Majalisar Dokokin Faransa Reuters/路透社
Talla

Tun lokacin harin Paris na 13 ga watan Nuwamba Faransa ke nazarin daukar matakan tsaro, kuma batun kwace shedar zama dan kasa ga duk wanda ke da alaka da ‘yan ta’adda na daga cikin sabbin sauye sauyen.

Gwamnatin Holland na san kafa sabbin tsare-tsate irin wadda kasar ta taba yi a baya lokaci yakin Algeria a shekarar 1995, saboda barazanar tsaro

Kazalika ana bukatar amincewar Malissar kasar kan batun tsaiwata dokar ta baci da ke karewa nan da kwananki 12 masu zuwa, da kuma amince da bukatar Hollande cikin kudin tsarin mulkin kasar

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da dama sun nuna adawarsu da wannan mataki na Faransa, yayin da duban mutane suka gudanar da gangami a ranar Assabar data gabata dan nuna adawarsu da sabbin tsare-tsaren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.