Isa ga babban shafi
Switzerland

Taron tattalin arzikin duniya a birnin Davos

A wannan alhamis an ci gaba da taron tattalin arziki na duniya a birnin Davos na kasar Switzerland inda a kowace shekara shugabannin manyan kasashe da ‘yan kasuwa ke tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arzikin duniya.

Taron Davos 2016
Taron Davos 2016 REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Manyan Kalubale da suka shafi tattalin arzikin duniya da suka hada da kwararar baki ‘yan gudun hijira zuwa Turai, hare-haren ta’addanci da kuma tabarbarewa tattalin arzikin China, na daga cikin muhimman batutuwan da taron na bana ya fi mayar da hankali a kai.

A wannan alhamis, akwai manyan baki da ke gabatar da jawabai ga mahalarta taron, da suka hada Firaministan Faransa Manuel Valls, da takwaransa na Girka Alexis Tsipras da na Birtania David Cameron.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.