Isa ga babban shafi
Spain

Jam’iyyar Rajoy ta sha kaye a majalisar Spain

Firaministan Spain Mariano Rajoy yace zai yi kokarin kafa sabuwar gwamnati bayan Jam’iyyarsa ta Peoples Party ta gaza samun rinjaye a majalisar kasar a zaben da aka gudanar a ranar Lahadi.

Firaministan Spain Mariano Rajoy
Firaministan Spain Mariano Rajoy Foto: Reuters
Talla

Jam’iyyar PP ta Firaminista Marino Rajoy da Jam’iyyar gurguzau, sun fuskanci babban kalubale daga wasu sabbin jam’iyyun siyasa guda biyu Podemos da Cuidadanos da suka shiga zaben.

Jam'iyyar PP ta samu nasara a zaben amma ta gaza samun rinjaye a Majalisa.

Yanzu gwamnatin Rajoy na neman hadin kai da wasu jam’iyyu domin kafa gwamnati saboda rashin samun rinjaye a majalisa.

Jam’iyyar PP ta samu sama da kashi 28 na kuri’un kasar abinda ya ba ta kujeru 123 daga cikin kujeru 350 na Majalisar.

Yayin da ya ke jawabi ga daruruwan magoya bayan sa Firaminista Rajoy na bukatar gwamnati da zata samu goyon bayan Majalisa don haka za su ci gaba da tattaunawa don ganin sun kulla yarjejeniyar kafa gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.