Birtaniya ta goyi bayan Faransa akan fada da IS
Shugaban Faransa Francois Hollande ya samu goyon bayan Firaministan Birtaniya David Cameron kan yakin da ya kaddamar da mayakan IS masu da’awar jihadi a duniya.
Wallafawa ranar:
Shugabannin sun gana ne a ranar Litinin kan jerin munanan hare haren da aka kai ranar Juma’a 13 ga watan Nuwamba a Paris.
Firamnistan Birtaniya David Cameron ya kai ziyara a Bataclan gidan cashewar da ‘Yan bindiga suka kashe mutane 90 tare da garkuwa da wasu a Paris.
Cameron ya bayyana goyon bayansa ga Hollande na kai wa mayakan IS hare hare ta sama a Syria.
Sannan Firamnistan ya bayyana cewa Birtaniya ma zata shiga cikin sahun kasashen da ke kai hari ta sama akan IS, kamar yadda Hollande ya tabbatar bayan ganawarsa David Cameron a Paris.
Cameron ya kuma ba Faransa damar yin amfani da sansanin jiragen sojinta a Cyprus domin shirya kai wa IS hari.
Nan gaba Hollande zai gana shugabannin kasashen Amurka da Rasha da Jamus kan yaki da mayakan IS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu