Isa ga babban shafi
Belgium

Belgium ta tsaurara tsaro

Firaministan Belguim Charles Michel ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro a yau Litinin domin kaucewa duk wani hari da yan ta’adda ke shirin kai wa a kasar.

Kasar Belgium ta tsauwala matakan tsaro don kaucewa hare haren ta'addanci
Kasar Belgium ta tsauwala matakan tsaro don kaucewa hare haren ta'addanci REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

Michel ya kuma bayyana cewar makarantu da tashoshin jiragen kasa za su kasance a rufe saboda bayanan da suka samu cewar ana shirya kai hare hare irin na Paris a Faransa.

Yanzu haka sojoji da ‘Yan sanda ne ke sintiri a Brussels don dakile duk wani hari na ‘Yan ta’adda.

Hare haren Paris da aka kai a ranar Juma’a 13 ga watan Nuwamba sun tayar da hankalin kasashen Turai.

Tuni Mayakan IS da ke da’awar Jihadi suka dauki alhakin kai hare haren.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci daukacin kasashen duniya su sanya hannu wajen yaki da ta’addancin da ke ci gaba da karuwa a duniya, bayan munanan hare haren da aka kai birnin Paris inda aka hallaka mutane kusan 130.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.