Isa ga babban shafi
Poland

Jam’iyyar da ke adawa da ‘Yan gudun hijira ta lashe zaben Poland

Jam’iyyar Law and Justice Party ta lashe zaben kasar Poland da aka gudanar a ranar Lahadi sakamakon matsayin Jam’iyyar da ke yakin zabe na kyamar baki ‘yan gudun hijira.

Jagoran Jam'iyyar Law and Justice  Jaroslaw Kaczynski, a Poland
Jagoran Jam'iyyar Law and Justice Jaroslaw Kaczynski, a Poland REUTERS/Pawel Kopczynski
Talla

Sakamakon zaben ya nuna cewar jam’iyar ta samu gagarumin rinjayen da za ta kafa gwamnati ba tare da hada kai da wata jam’iya ba.

Wanan shi ne karo na farko da wata jam’iya za ta kafa gwamnati ba tare da hadin kai ba a tarihin siyasar kasar Poland kamar yadda jagoran tafiyar Jam’iyyar Jaroslau Kaczynski ya bayyana.

Tuni dai Firaminista Ewa Kopacz ta amsa shan kaye a zaben na Poland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.