Isa ga babban shafi
Faransa-Air Frace

Gwamnatin Faransa na fatar gani an kawo karshen rikicin Air France

A ranar Alhamis mai zuwa ne a Faransa, za ‘a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin magabatan kamfanin Air France da kungiyoyin kwadagon kasar. Gani ta yada rikicin ke ci gaba da zazzafa, Gwamnatin kasar ta tsoma bakin ta domin gani an warware wanan matsalla. 

Kamfanin Air France
Kamfanin Air France REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Kamfani jiragen saman kasar Faransa na Air France ya sanar a baya da cewa zai salami ma’aikata 2900 a shekara ta 2016 a wani shirin sa na samar da daidaito dama ceto kamfani .
Shugaban kamfani na Air France Alexandre de Juniac a jiya lahadi ya bayyana cewa kamfani da yake shuganbata zai salami akala mutane 1.000 a karon farko ,banda haka kamfani zai bulo da wasu hanyoyi na gani ma’aikata 1900 masu bukata sun fice daga kamfani na Air France a zagaye na biyu.

Idan aka yi tuni a ranar 5 ga watan Oktoban nan ne ma’aikantan Air France a fusace suka yayaga tufafin Xavier Broseta shugaban dake kula da wani sashe na Air France.
Gwamnatin ta damu ainu da al’amarin dake faruwa a Air France,
Francois Hollande Shugaban kasar ta Faransa ya aike da sako zuwa masu ruwa da tsaki a wanan kamfani na Air France dama ma’aikantan.
Hollande ya na mai fatar gani an kawo karshen wanan rikici dake neman kawo durkushewa kamfanin Air France.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.