Isa ga babban shafi
Belarus-Rasha

EU ta amince a cire wa kasar Belarus takunkunmi

Ministocin Kungiyar kasasen Turai sun amince a cirewa kasar Belarus takunkumin da aka kakaba mata sakamakon nasarar da shugaban kasar Alexander Lukashenko ya samu a zaben kasar.

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko 路透社
Talla

Ministan Faransa dake kula da ayyukan kungiyar Harlem Desir ya shaidawa manema labarai cewar ministocin kungiyar sun amince a cire takunkumin nan da watannin hudu masu zuwa.

Ita dai kungiyar ta sanya takunkumin tafiye tafiye da kuma rufe asusun ajiyar Lukashenko da kuma jami’an kasar 170 da kungiyoyi 14.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan Lukashenko ya yi afuwa ga fursunonin siyasa na karshe a kasar ta Belarus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.