Isa ga babban shafi
Macedonia

Baki dubu 10 sun shiga Macedonia a cikin awanni 24

‘Yan Sanda a Macedonia sun ce Bakin haure da ‘Yan gudun hijira dubu 10 ne suka shiga kasar a yau Alhamis a cikin sa’oi 24 daga Girka, al’amarin da ya tayar da hankulan hukumomin kasar saboda kan-kantarta.

Bakin hauren da ke neman shiga Kasar Macedonia.
Bakin hauren da ke neman shiga Kasar Macedonia. REUTERS/Ognen Teofilovski
Talla

Tun farkon watan Satumban da ya gabata, ake samun karuwar bakin haure da ke shiga kasar a kullum, musamman wadanda ke tsere wa rikicin gabas ta tsakiya.

Duk da hasashen da hukumomi da kungiyoyin agaji ke yi na samun ragin bakin da ke kutsa kai zuwa Turai saboda yanayin bazara da hatsarin tsallaka teku daga Turkiya zuwa Girka, a yanzu akalla Bakin haure dubu 3 suka mutu a kokrinsu na tsallaka tekun Mediterranean a wannan shekarar.

Sai dai mai magana a madadin ministan cikin gidan kasar ta Macedonia, Ivo Kotevski ya yi mamakin wannan alkalluma a sa’oi 24 cikin Karamar kasar kuma akwai yiwuwar alkallumar su zarce haka.

Batun da ke zuwa a dai-dai lokacin da Ministocin Turai ke cewa ya kamata a dau matakan fara mayar da Bakin da suka rasa mafaka a kasashen saboda yawansu.

Akalla dai yanzu Bakin haure kusan dubu 600 ne suka shiga Jamus a cikin watanni 9 kamar yadda hukumomin kasar suka ce, kuma kashi 1 cikin 3 duk 'Yan Syria ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.