Isa ga babban shafi
Australia

Amfani da leda na cutar da tsuntsayen ruwa

Wani rahoton bincike da aka wallafa yace tsuntsaye sun koma cin leda saboda yadda ake zubar da shara a ruwa, rahoton ya kara da cewa tsuntsaye zasu ci gaba da mutuwa saboda cin leda da yawa muddun aka gagara magance matsalar zubar da shara a ruwa.

Ledoji a bakin Tekun India
Ledoji a bakin Tekun India PAL PILLAI / AFP
Talla

Rahoton wanda cibiyar binciken kimiya a Australia ta gudanar, ya bayyana cewa tsuntsaye sun koma cin leda a teku kuma rahoton ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2050 kusan kashi 90 na tsuntsaye sun ci leda.

Rahoton yace cin ledar barazana ce ga lafiyar tsuntsaye, kuma idan suka ci da yawa zasu mutu.

An wallafa rahoton ne bayan masana sun gudanar da bincike akan na’uin tsuntsayen ruwa 135 daga shekarar 1962 zuwa 2012 da aka gano sun koma cin leda da nufin neman abinci a teku.

Binciken ya bayyana cewa Zuwa 2010 adadin tsuntsayen ruwa da suka ci leda sun kai kashi 80, kuma adadin zai ci gaba da kruwa a shekaru masu zuwa.

An Fara amfani da leda dai tun a 1950, kuma wannan ya kara haifar da gurbatar muhalli a kasashen duniya.

Binciken ya auna cewa akwai adadin leda 580,000 a duk nisan kilomita a tekunan duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.