Isa ga babban shafi
Hungary

Za'a tattaunawa matsalar 'yan ci-rani da suka shiga Hungary

Shugaban hukumar kungiyar Tarayyar Turai, Jean Claude Juncker zai gana da Firaiministan Kasar Hungary Viktor Orban domin tattauna yadda za’a taimakawa kasar ta Hungary shawo kan matsalar kwararar bakin haure cikin kasar.

'Yan ci-rani a Hungary
'Yan ci-rani a Hungary REUTERS/Laszlo Balogh
Talla

Hukumomin kasar ta Hungary sun dau matakin hana daruruwan bakin shiga tashar jirgin kasa na birnin Budapest ne a safiyar yau domin hana su kutsawa cikin kasashen Autsria da Jamus duk da dai a farko sun budewa wasu daga cikin su hanya.

Matakin dai ya matukar bakanta ran ‘yan ciranin inda wasu daga cikinsu suka zazzauna a kasa cikin kunci.

A ranar Alhamis mai zuwa shugaban hukumar tarayyar turai Jean Claude Juncker zai karbi bakwancin Firaiminstan Hungary Viktor Orban domin tattaunawa akan matsalar kwararar bakin da Hungary ke fama da ita.

A yanzu kuma hukumar ta shirya baiwa Hungary tallafin kudadde kusan Euro miliyan 8 domin taimaka mata wajan daukar dawainiyar baki sama da dubu Hamsin wadanda akasarin su ‘yan kasar Syria ne da suka tserewa rakicin kasar su.

Alkalumma sun nuna cewa kimanin bakin haure dubu 350 ne suka dau kasadar tsallaka tekun Mediterranean domin shiga kasashen dake nahiyar Tuari a cikin wannan shekarar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.